Home Labarai Shugaba Buhari Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekara 15 Kan Gadon...

Shugaba Buhari Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekara 15 Kan Gadon Sarauta

42
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III murnar cika shekara 15 kan gadon sarauta.

Shugaban,cikin sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana Sarkin a matsayin “mai gina zaman lafiya da jajircewa ga aikinsa, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata rayuwar al’umma.”

Buhari ya yi wa Sarkin Musulmi fatan samun wasu shekaru masu yawa kan matsayinsa tare da ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da ƙabilu a sassan Najeriya.