Home Home Kotun Koli Ta Ce An Yi Yunkurin Kashe Mai Shari’a Mary Odili

Kotun Koli Ta Ce An Yi Yunkurin Kashe Mai Shari’a Mary Odili

96
0


Kotun ƙolin ta bayyana samamen da aka kai wa ɗaya daga cikin manyan alƙalanta Mary Odili a ranar Juma’a a matsayin “wata manufa ta yunƙurin halaka ta ko kuma yi mata lahani.”

Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gudanarwar Kotun ƙolin Festus Akande ya fitar ta danganta farmakin da manufar yaƙi da halaka ta yana mai cewa “wasu ɗauke da makamai da ake tunanin jami’an tsaro daga hukumomin gwamnati daban-daban waɗanda da alama sun zo ne da nufin kashe wadda suke nema da sunan samun sammacin gudanar da bincike da ba shi da tushe.”

A ranar Juma’a ne wasu jami’an tsaro suka yi wa gidan Mary Odili matar Peter Odili tsohon gwamnan jihar Rivers dirar mikiya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Hukumar EFCC da DSS da ministan shari’a dukkaninsu sun nesanta kansu daga kai samame gidan Mai shari’ar.

Bayan ta yi Allah wadai, Kotun Kolin ta danganta farmakin da irin wanda ta ce jami’an tsaron farin kaya sun taɓa kai wa gidajen wasu alƙalai ciki har da nata guda biyu a Abuja a shekarar 2016.