Home Labaru Shugaba Buhari Ya Taya Alhazan Nijeriya Murnar Kammala Aikin Hajji

Shugaba Buhari Ya Taya Alhazan Nijeriya Murnar Kammala Aikin Hajji

245
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya Alhazan Nijeriya murnar bikin babbar sallah da kuma kammala aikin hajjin bana a kasa mai tsarki.

Buhari ya kuma yi alhini tare da jajenta wa ‘yan’uwa da ma’aikatan hukumar Alhazai game da rasuwar wasu daga cikin mahajjatan Nijeriya a kasar Saudiya.

Karanta Labaru Masu Alaka: Maniyyatan Nijeriya Shida Sun Rasu A Kasar Saudiyya – NAHCON

Hukumar Alhazai ta Nijeriya dai ta bayyana cewa, a bana musulmin Nijeriya 45,000 ne su ka gudanar da aikin hajji a kasar Saudiyya.

Shugaban hukumar na kasa Abdullahi Muhammad ne ya wakilci shugaba Buhari a wani taro da aka gudanar a birnin Mina da ke kasar Saudiyya.

Shugaba Buhari ya bukaci mahajjatan Nijeriya su tsananta addu’o’in neman magance kalubalen da Nijeriya ke fuskanta, musamman tabarbarewar tattalin arziki, da rashin tsaro da tsananin adawar siyasa.