Home Labaru An Ce Fadar Shugaban Kasa Ta Salami Sanata Ita Enang Daga Mujkamin...

An Ce Fadar Shugaban Kasa Ta Salami Sanata Ita Enang Daga Mujkamin Sa

334
0

Rahotanni na cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya salami Sanata Ita Enang daga mukamin san a mai bas hi shawara a kan harkokin majalisar dattawa.

Yayin da aka nemi jin ta bakin sa game da lamarin, Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya nemi ‘yan jarida su tuntubi Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Garba Shehu, ya ce Sakataren gwamnatin tarayya ne zai yi magana a kan halin da a ke ciki.

Karanta Labaru Masu Alaka: Majalisar Bata Sanar Da Buhari Komai Ba

A na si bangaren, Sanata Ita Enang bai amsa kiran da ‘yan jarida su ka yi masa domin jin ta bakin sa ba.

A Ranar 11 ga watan Agusta ne, rahotanni su ka rika yawo cewa  shugaba Buhari ya sauke Ita Enang daga matsayin sa na mai taimaka masa a kan sha’anin majalisar dattawa.

Ita Enang dai ya taba zama dan majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar PDP, amma ana daf da zaben shekara ta 2015 ya sauya sheka zuwa APC.