Home Labaru Shugaba Buhari Ya Sanya Hannu A Kan Sabuwar Dokar Zabe

Shugaba Buhari Ya Sanya Hannu A Kan Sabuwar Dokar Zabe

64
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa hannu a kan sabuwar dokar zabe, yayin wani takaitaccen zama tare da Shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilai a fadar sa da ke Abuja.

Da ya ke jawabi lokacin da ya ke sanya wa dokar hannu, Buhari ya bukaci ‘yan majalisar su hanzarta yin gyara ga sashe na 84, wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko na ‘yan takara.

Shugaba Buhari, ya ce sabuwar dokar za ta ƙara inganta harkar zaɓe ta hanyar tabbatar da an yi abubuwa a bayyane ba tare da nuƙu-nuƙu ba a lokacin zaɓen, da kuma rage abubuwan da za su sa ‘yan takara su yi ta ƙorafe-ƙorafe.

Ya ce wannan ƙoƙarin na sa hannu a kan dokar zaɓen, ya na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin su na ƙara buɗe hanya domin gudanar da sahihin zaɓe mai inganci.

Shugaba Buhari, ya ce babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa da zai iya zama wakilin masu zaɓe ko kuma a zaɓe shi yayin babban taron jam’iyya don ya tsaya takarar zaɓe.