Jami’an Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, sun kama wasu fitattun mawaka biyu da wasu mutane hudu dauke da kwayoyi a wani samame da su ka kai a birnin Legas.
Hukumar ta shaida wa manema labarai cewa, an samu wasu nau’ukan tabar wiwi a hannun mawakan, wadanda su ka hada da Zinoleesky da Mohbad da wasu mutane hudu da ake zargi.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an gama bincike.
Mohbad da Zinoleesky dai shahararrun mawakan Gambara ne na zamani, wadanda ake fitar da wakokin su a fadin nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.














































