Home Labaru Farashin Kananzir: Abin Da Ya Sa Ya Yi Tashin Gwauron Zabo –...

Farashin Kananzir: Abin Da Ya Sa Ya Yi Tashin Gwauron Zabo – NNPC

262
0
Kamfanin NNPC
Kamfanin NNPC

Kamfanin Man Fetur na NNPC, ya bayyana dalilin tashin farashin Kananzir, cewa hakan ya faru ne saboda matsin-lambar yawan bukatar sayen sa daga masu sayarwa.

Kakakin kamfanin NNPC Ndu Ughamadu ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja, inda ya ce saida kananzir ba tare da bin ka’ida ba ne ya haifar da Karin farashin tsakanin mai saye da mai sayarwa.

Ya ce kananzir ba ya da tsauraran matakan sa-ido na ka’idar saida shi kamar yadda ake yi wa man fetur, shi ya sa farashin sa ya karu.

Mista Ndu ya cigaba da cewa, yawan bukatar sayen kananzir da ake yi ke kara sa ya na kara tsada a hannun masu sayarwa.

Wani binciken da aka yi ya nuna cewa, gidajen man da ke wajen Birnin Abuja su na saida litar kananzir daya a kan naira 400 zuwa 500.

Ya ce akasarin masu amfani da kananzir duk a hannun ‘yan gada-gada ko gefen titi su ke sayen sa, ya na mai shan alwashin cewa kamfanin NNPC zai cigaba da wadatar da kasar nan da isasshen man fetur da kananzir.