Home Labaru Shugaba Buhari Ya Karawa Dogarinsa Mukami

Shugaba Buhari Ya Karawa Dogarinsa Mukami

88
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa dogarinsa, Laftanar Kanal YM Dodo kwalliyar anini ta karin girma da ya samu zuwa matsayin Kanal.

Hotunan da Fadar Shugaban Kasa ta yada sun nuna shugaba Buhari da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo sun sa wa Laftanar Kanal Dodo da ya zama Kanal aninin ne gabanin taron Majalisar Tsaro da ya gudana a nan Abuja.

Bayanai sun ce Buhari ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis din nan.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Janar Babagana Monguno da Shugaban Hukumar Leken Asiri (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Sauran sun hada da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Lcuky Irabor da kuma Manyan Hafsoshin Rundanar Sojojin Ruwa, Kasa da na Sama.