Gwamnaonin Arewa maso yammacin Najeriya sun bukaci a dauki matakai masu tsauri domin kare rushewar gine gine.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne sa’ilinda suka kai ziyarar jaje ga gwamnatin Jihar Lagos Babajide Sanwo Olu.
Tawagar Gwamnonin da ta hada da wasu ‘yan majalisar dokoki ta kasa sun nuna matukar damuwar su akan yadda rushewar Ginin da haddassa mutuwar mutane da dama.
Azantawarsa da manema labarai Gwamnan Jihar Kano Abdullahhi Umar Ganduje yace sun ziyarci Jihar Legas ne domin jajantawa ‘yan uwan wadanda lamarin ya rutsa dasu dama Al’ummar Jihar Legas baki da.
Anasa jawabin Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari yace kasancewar babu yadda za’a iya kaucewa gina dogayen benaye a Jihar Legas, akwai bukatar a rika kiyayewa tareda bin ka’ida yayin yin gini.
Daga bisani tawagar ta nuna gamsuwa akan matakan da Gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu ya dauka akan lamarin.
Idan ba’a manta ba dai a kwanakin baya ne wani Gini mai hawa 21 ya ruguje a Birnin Legas inda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
You must log in to post a comment.