Home Labaru Kasuwanci Kara Kudin Man Fetur Zai Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Mawuyacin Hali –...

Kara Kudin Man Fetur Zai Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Mawuyacin Hali – Shehu Sani

175
0

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana fargaba haln da zasu shiga bayan cire tallafin man fetur baki ɗaya a shekara mai zuwa.

Azantawarsa da kafar yada labarai ta BBC tsohon Dan majalisar Dattijai daga Jihar Kaduna Sanata Shehu Sani ya ce matakin cire tallafin dari bisa dari jefa rayuwar ‘yan Najeriya cikin garari. 

Tun bayan samun sanarwar gwamnatin tarayya na tabbatar da cire tallafin mai baki ɗaya cewa a farkon shekarar 2022 aka fara tafka muhawara kan matakin.

Gwamnati dai a ta bakin, Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta ce gwamnati ba ta sanya tallafin man fetur da lantarki cikin tsare-tsaren kuɗinta na 2022 ba.

Sannan ta shaida cewa a maimakon tallafin mai za a baiwa ‘yan Najeriya masu karamin karfi tallafin sufuri na naira dubu biyar-biyar a kowanne wata.

Leave a Reply