Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar tsarin zamani na e-Naira, a daidai lokacin da Nijeriya ke kokarin cin moriyar samfurin kudin da ake kira cryptocurrency.
Da wannan tsarin dai, Nijeriya ta shiga sahun kasashe irin su China da da su ka fara amfani da kudin bisa jagorancin manyan bankunan su.
Yayin kaddamar da shirin ta yanar gizo, shugaba Buhari ya ce Nijeriya ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta fara amfani da wannan nau’in kudi, wanda ya ce zai habaka kasuwanci da cinikayya a tsakanin kasashe.
Masana tattalin arziki sun ce, ana sa ran sabon nau’in kudin na e-Naira zai saukaka tare da gaggauta hada-hadar kasuwanci tsakanin Nijeriya da kasashen duniya.














































