Home Labaru Harin Uganda: Shugaba Museveni Ya Ce Akwai Yiwuwar Na Ta’addanci Ne

Harin Uganda: Shugaba Museveni Ya Ce Akwai Yiwuwar Na Ta’addanci Ne

5
0
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya siffanta harin bam da ya kashe mutum ɗaya a Kampala babban birnin ƙasar da cewa akwai yiwuwar na ta’addanci ne.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya siffanta harin bam da ya kashe mutum ɗaya a Kampala babban birnin ƙasar da cewa akwai yiwuwar na ta’addanci ne.

An kai harin ne a wani shahararren wajen cin abinci da ke yammacin birnin a ranar Asabar kuma mutum bakwai ne suka jikkata a harin.

An tsaurara tsaro a wurin da lamarin ya faru yayin da ‘yan sanda ke ƙoƙarin gano hujja.

Waɗanda suka shaida lamarin sun faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa mutum biyu ne suka shiga wurin da wani abu a cikin kwalba ƙunshe a jaka sai dai har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da nau’in abin fashewar ba.

Hukumomi a Ugnada na zargin ƙungiyar ‘yan aware ta ƙasar Congo mai suna ADF da shirya harin ta’addancin.