Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Ce An Kama Fursunoni 500 Da Su Ka Tsere

Gwamnatin Tarayya Ta Ce An Kama Fursunoni 500 Da Su Ka Tsere

13
0

Ma’aikatar harakokin cikin gida ta Nijeriya, ta ce an sake kama fursunoni akalla 500 da su ka tsere daga gidan yarin jihar Oyo.

Yayin da ya kai ziyara gidan yarin, Ministan harakokin cikin gida Rauf Aregbesola, ya ce ya zuwa yanzu an sake kama fursunoni 446 daga cikin sama da 800 da su ka tsere.

Rauf Aregbesola, ya ce akwai fursunoni 69 da ba su tsere daga  gidan yarin ba.

Daruruwan fursunoni ne su ka tsere daga gidan yarin Abonlogo a jihar Oyo, bayan ‘yan bindiga sun kai farmaki a gidan yarin, inda su ka kashe jami’in soji ɗaya da ɗan banga ɗaya.