Home Labaru Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Tarin Mutane Birnin Gwari

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Tarin Mutane Birnin Gwari

132
0

‘Yan bindiga a Najeriya sun tare tawagar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari inda suka kwashe mutane da dama suka gudu da su cikin daji.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar yau lokacin da matafiyan ke kan hanyar su ta zuwa Kaduna bayan sun bar Birnin Gwari.
Wani shugaban al’umma Muhammadu Umaru ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar daga cikin wadanda aka kwashe akwai makotan sa guda 4 a cikin tawagar motoci 20 dake samun rakiyar jami’an Yan Sanda.
Umaru yace akalla matafiya 70 ke cikin tawagar daga garin Udawa, yayin da yace akwai kuma Karin wasu mutane daga wasu garuruwa dake tsakanin Udawa da Buruku.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda su gudu cikin daji sun kira ‘yan uwan su inda suka shaida musu abinda ya faru.
Ya zuwa wannan lokaci, rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna bata tabbatar da aukuwar lamarin ba tukuna.