Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa Al’ummar Jihar Kano da kuma gwamnatin jihar bisa hatsarin kwale-kwalen da ya auku a Ƙaramar Hukumar Bagwai inda fiye da mutum 20 suka rasa rayukan su.
A wani saƙo da ya aike wa gwamnatin da jama’ar jihar, shugaba
Buhari ya ce hukumomin gwamnatin tarayya za su bayar da
gudunmawar da ta dace a daidai lokacin da ake ci gaba da
neman waɗanda suka ɓace yayin hadarin.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai kwale-kwalen ya nutse dauke
da fasinjojin yawancin su yara ƙanana kuma ɗaliban Islamiyya.
Jami’an ƴan sanda da ƴan kwana-kwana da masunta ne ke ci
gaba da aikin ceton wadanda suka saura da nunfashi da kuma
gawawwaki.
You must log in to post a comment.