Home Labaru Annobar Korona: Mutane Miliyan 247 Zasu Bukaci Tallafi A Shekarar 2022 –...

Annobar Korona: Mutane Miliyan 247 Zasu Bukaci Tallafi A Shekarar 2022 – MDD

134
0

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa bukatar agaji zai karu a fadin Duniya a shekarar 2022 sakamakon karuwar annobar korona da matsalar sauyin yanayi da kuma rikice rikice.


Hukumar jinkai ta Majalisar tayi hasashen cewar akalla mutane miliyan 247 a duniya zasu bukaci taimakon gauggawa a badi, adadin da ya zarce na wannan shekarar da kashi 17 cikin 100.


Wannan adadi ya nuna cewar a cikin ko wadanne mutane 29 dake duniya, mutum guda zai bukaci agaji a shekara mai zuwa, adadin da ya zarce na shekarar 2015.


Shugaban hukumar jinkan Martin Griffiths yace ba’a taba samun yawan mutanen dake bukatar agajin da ya kai na wannan lokaci ba, kuma samar musu da agajin ba’a abu ne mai dorewa ba, amma kuma ya zama dole ayi.
Gidauniyar taimakawa mabukatar ta Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin agaji sun ce ana bukatar Dala biliyan 41 domin tallafawa mutane miliyan 183 a kasashen duniya 63 a shekara mai zuwa, adadin da ya zarce Dala biliyan 35 da aka bukata a cikin wannan shekarar ta 2021.

Leave a Reply