Home Labaru Shugaba Buhari Ya Jajanta Wa Biden

Shugaba Buhari Ya Jajanta Wa Biden

12
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa takwaran sa na Amurka  Joe Biden kan mutuwar tsohon ministan harkokin wajen kasar Colin Powell.

Sanarwar wadda mataimaki na musamman ga Shugaban kasa kan yada labarai Garba Shehu ya fitar, ta bayyana marigayi Colin Powell a matsayin mutun nagari da duniya ta yi alfahari dashi.

Hakama Shugaba Buhari ya bayyana marigayi Powell a matsayin ba’amurike dan asalin Afrika na farko da ya rike mukami mafi girma a harkar tsaron Amurka, kuma ya yi amfani da matsayin sa wajen kulla kyakkyawar alaka da kasashen waje.

Shugaban kasa ya kuma ce duniya ba za ta mance da rawar da Colin Powell ya taka ba wajen yaki da cutar shan inna da kuma takaita yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a nahiyar Afrika.

Collin Powell ya mutu ne ranar Litinin yana da shekara 84 a duniya.