Home Labaru Gwamnatin Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 863

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kashe Naira Biliyan 863

15
0

Gwamnatin Najeriya za ta kashe tsabar kudi Naira biliyan 863 wajen gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma na karshen shekara.

Shirye-shiryen dai na musamman ne da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo da su da nufin rage wa ‘yan Najeriya radadin talauci.

Shirin National Social Investments Programmes (NSIP) da ya kunshi shirin N-Power da Conditional Cash Transfer Programme (CCT), da kuma shirin raba basussuka ga kananan yan kasuwa zai lakume kudi har Naira biliyan 410.

Za a kuma kashe karin Naira biliyan 300 kan wasu shirye-shiryen na daban ga al’umma.

Tun a shekarar 2016 ne gwamnatin shugaba Buhari ta bullo da shirye-shiryen tallafa wa yan Najeriya don rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki.

Kuma a 2020 abubuwa sun dada nauyi ga yan Najeriya bayan bullar annobar korona, da ta yi illa ga tattalin arziki.