Home Labaru Kasuwanci Gwamnati Ta Soke Hukumomin DPR Da PPPRA Da PEF

Gwamnati Ta Soke Hukumomin DPR Da PPPRA Da PEF

17
0

Gwamnatin Najeriya ta ce ta soke hukumomi uku a ɓangaren man fetur kamar yadda sabuwar dokar man ta tanada.

Dokar, wadda aka sa hannu a kanta a watan Agusta ta buƙaci a soke hukumomin DPR da PPPRA da PEF.

A halin da ake ciki dai an kafa wasu sabbin hukumomi biyu da za su maye gurbin su, wato Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority da Nigerian Upstream Regulatory Commission, kuma hukumomin biyu za su sa ido ne kan hakar mai da sarrafa shi a Najeriya.

Ƙaramin ministan man fetur, Timipre Sylva ya tabbatar da kafa sabbin hukumomin da fara aikin su inda ya ƙaddamar da hukumar darektocin sabbin hukumomin a nan Abuja ranar Litinin.

Timipre Sylva ya bayyana cewa gwamnati za ta kare ayyukan ma’aikatan tsoffin hukumomin uku da aka soke duk da cewa an sallami shugabannin su daga mukaman su.