Home Labarai Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro A Abuja

Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro A Abuja

101
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar tsaro ta kasa a fadar sa da ke Abuja.

Mai taimaka wa shugaban kasa a kan kafafen sada zumunta Buhari Sallau ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Tuwita.

Taron dai ya samu halartar Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno.

Sauran sun hada da Babban Hafsan tsaro na ƙasa Janar Lucky Irabor, da shugaban sojin ƙasa Laftanar Janar Farouk Yahaya, da shugaban sojin ruwa Vice Admiral Awwal Gambo da shugaban rundunar sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao.

Wasu daga cikin mahalarta taron kuma akwai shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alƙali Baba, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Yusuf Bichi, da kuma daraktan hukumar tsaron fasaha NIA Ahmed Rufa’i Abubakar.