Home Labarai Kotu Ta Karbi $61,400 Matsayin Shaidar Badakalar Abba Kyari

Kotu Ta Karbi $61,400 Matsayin Shaidar Badakalar Abba Kyari

14
0

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta karbi tsabar kudi Dala dubu 61 da 400 da aka gabatar mata a matsayin shaidar hancin da ake zargin Abba Kyari ya ba jami’an Hukumar Yaki da Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA.

Alkalin Kotun Mai Shari’a Emeka Nwite, ya amince da hakan ne a zaman kotun na ranar Larabar da ta gabata, bayan hukumar NDLEA ta gabatar da shaidar ta ta hannun mai tuhuma na uku Peter Joshua.

Yayin gudanar da shari’ar, Joshua wanda babban jami’in hukumar NDLEA ne a ofishin sur da ke Legas ya shaida wa kotun cewa, a ranar 25 ga Janairu aka mika ma shi kudaden bayan ya kammala bincike a kan zaman kudin shaida.

Hukumar NDLEA ta yi ikirarin cewa, ta na da bidiyon yadda Abba Kyari ya ke tayin bada toshiyar bakin Dala dubu 61 da 400 domin hana yin gwajin wasu miyagun kwayoyi da da aka kama masu nauyin akalla kilogram 17 da rabi.

Kwayoyin dai wani bangare ne na hodar iblis mai nauyin kilogram 21.35, wadda aka kama an shigo da ita Nijeriya ta Babban Filin Jirgi na Akanu Ibiam da ke Inugu.