Home Labaru Kasuwanci Gwamnatin Buhari Za Ta Kashe Tiriliyan N6.72 A Kan Tallafin Man Fetur A...

Gwamnatin Buhari Za Ta Kashe Tiriliyan N6.72 A Kan Tallafin Man Fetur A 2023

9
0

Gwamnatin tarayya, ta ce za ta samar da kudin tallafin man fetur da ya kai naira tiriliyan 6 da biliyan 72 a shekara ta 2023.

Ministar kudi da kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed ta bayyana haka a Abuja, inda ta ce gwamnati ta kiyasta cewa, za ta samar da kudaden ne ta hanyoyi biyu kamar yadda ya ke kunshe a cikin kasafin kudin Nijeriya.

A karkashin hanya ta farko, ministar ta ce an kiyasta cewa, za a samar da tallafin tiriliyan 6 da biliyan 72 a shekara ta 2023.

Ministar ta kara da cewa, kamfanin NNPC ne zai samar da kudaden a madadin gwamnatin tarayya.