Home Labaru Shugaba Buhari Ya Fitar Da Jerin Sunayen Ministocin Sa

Shugaba Buhari Ya Fitar Da Jerin Sunayen Ministocin Sa

794
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fitar da jerin sunayen ministocin sa 43 da ya aike wa Majalisar Dattawa domin tantance su.

Da misalin karfe 11 na safiyar Talatar nan ne, shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ya karanta sunayen ministocin a zauren Majalisar.

Karanta Labaru Masu Alaka: Masu Kishi Da Rikon Amana Zan Zaba A Sabbin Ministoci – Buhari

Sanata Ahmed Lawan, ya kuma bada tabbacin fara zaman tantance  sabbin ministocin a ranar Laraba, 24 ga watan Yuli na shekara ta 2019.

Wasu daga cikin sabbin ministocin da shugaba Buhari ya aike wa majalisar kuwa sun hada da Godswill Akpabio, da Timipre Sylva da Ali Isa Pantami Lai Mohammed da Babatunde Fashola da Rotimi Amaechi da sauran su.