Home Labaru Sakin El-Zakzakky: Kawunan ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Rarraba

Sakin El-Zakzakky: Kawunan ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Rarraba

644
0

An samu rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan majalisar wakilai, bayan dan majalisa Hembe ya bukaci gwamnatin tarayya ta bi umarnin kotu na sakin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Haka kuma, ‘yar majalisa Linda Ikpeazu ta bukaci gwamnatin jihar Kaduna ita ma ta bi umarnin kotu a kan batun sakin Malam Ibrahim El-Zakzaky.

Sai dai bayan shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya yi shelanta bukatar hakan ga sauran ‘yan majalisar ta hanyar jefa kuri’ar jin ra’ayoyi a kan bukatar ‘yan majalisar biyu, sai muryar wadanda ba su amince da hakan ba ta yi rinjaye.

Kin amincewar mafi yawan ‘yan majalisar ya sa masu goyon bayan kudirin yin tirjiya, lamarin da ya tilasta shugaban majalisar ya bukaci masu goyon bayan kudiri ko adawa da shi su ware bangare guda domin tantance masu rinjiaye.

Amma jim kadan bayan ‘yan majalisar sun fara warewa, sai Gbajabiamila ya bukaci dogaran majalisa su umarci duk wanda ba dan majalisa ba ya fita domin a kada kuri’a a kan kudirin cikin sirri, lamarin da ya wasu ‘yan majalisar su ka fice daga zauren majalisar.