Home Labaru Rahoto: Talauci Ya Yi Wa Al’ummar Afrika Katutu

Rahoto: Talauci Ya Yi Wa Al’ummar Afrika Katutu

213
0

Wata  sabuwar kididdigar masana tattalin arzikin kasa da kasa, ta nuna cewa adadin mutanen da ke fama da matsanancin talauci a nahiyar Afrika ya kai matakin Ha’ula’i.

Masanan sun kara da cewa, matsalar za ta ci gaba da tsananta, saboda saurin karuwar yawan al’umma da nahiyar za ta fuskanta a shekaru 10 dake tafe.

Sabon shugaban bankin duniya David Malpass,  ya ce kalubalen da ake fuskantar a nahiyar ta Afrika ba karami ba ne, dan haka akwai bukatar ware kudade masu yawan gaske da kuma tsara hanyoyin samar da guraben ayyukan yi, da kuma ababen more rayuwa domin tafiya dai-dai da karuwar yawan al’umma a Afrika.

Sakamakon wani bincike da bankin Duniya ya yi a shekarar 2015, ya nuna cewa matsalar talauci ta ja baya a sassan duniya da akalla kashi 10 cikin 100, sai dai a Afrika abin ba haka yake ba, domin a shekara ta 2015, rabin wadanda ke fama da matsanancin talauci a duniya na zaune ne a Nahiyar.

Hasashen masana ya ce nan da shekara ta 2030, kusan mutane 9 daga cikin 10 dake kangin talauci a duniya za su fito ne daga Afrika.

Hakan ce ta sa Asasun Bada lamuni na duniya wato IMF, ya bayyana bukatar samar da guraben ayyunkan yi akalla miliyan 20 a Nahiyar, domin rage yawan al’ummar Nahiyar Afrika dake cikin kangin talauci wanda adadinsu ya kai miliyan 700.