Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga daliban jami’o’in Nijeriya su kara hakuri, ya na mai cewa gwamnati ta na bakin kokarin ganin an kawo karshen yajin aikin da malamai ke yi.
Tun a watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami’o’in ta shiga yajin aiki, inda ta ke zargin gwamnati da abin da ta kira rashin kulawar da ta ke nunawa wajen neman maslaha a kan lamarin.
Yayin wani taron karrama masu hazaka na kasa da aka yi a Abuja, shugaba Buhari ya yi kira ga daliban su kara hakuri a kan halin da su ke ciki.
A cikin wata sanarwa da Kakakin sa Femi Adesina ya raba wa manema labarai, Buhari ya ce gwamnati ta na bakin kokarin ta wajen ganin ta lalubo bakin-zaren matsalar tare da yin la’akkari da iyakar karfin da su ke da shi.
Shugaba Buhari, ya kuma yi kira ga kungiyar ASUU ta duba halin da daliban ke ciki ta janye yajin aikin.
Ya ce tuni ya ba shugaban ma’aikatan fadar sa da ministocin kwadago da na ilimi da minister kudi umarnin su
yi gaugawar gayyato duk masu ruwa da tsaki a kan teburin sulhu don a duba bukatun kungiyar ta ASUU.














































