Home Labarai Buhari Ya Umarci Gwamnan Cbn Ya Sauka Daga Mukamin Sa

Buhari Ya Umarci Gwamnan Cbn Ya Sauka Daga Mukamin Sa

33
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emifiele ya sauka daga mukamin sa sakamakon bayyana aniyar sa ta tsayawa takara a zaben shekara ta 2023.

Rahotanni sun ambato yadda sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya mika bukatar hakan ga daukacin mukarraban gwamnati da ministocin da ke shirin tsayawa takara ciki har da Emifiele.

Wasikar dai ta na dauke da sabon cewa, wajibi ne ministoci da shugabannin hukumomi da jakadu baya ga masu rike da mukaman siyasa su gaggauta sauka daga kujerun su kafin nan da ranar 16 ga watan Mayu.

Godwin Emefiele dai ya shiga tsaka mai wuya ne, sakamakon caccakar da ta yi ma sa yawa tun bayan da hazakar wasu kungiyoyi su ka karo-karo tare da saya masa Fom na takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya bukaci shugaba Buhari ya sauke gwamnan babban bankin da karfin tuwo, matukar ya ki amincewa ya sauka daga kujerar sa kamar yadda aka bukata.