Home Labaru Shugaba Buhari Ya Aike Da Tawaga Don Yi Wa Jama’ar Jihar Katsina...

Shugaba Buhari Ya Aike Da Tawaga Don Yi Wa Jama’ar Jihar Katsina Jaje

636
0

Fadar masarautar Katsina ta fitar da wata sanarwar, sakon jaje ga daukacin jama’arta kan ibtila’in kashe-kashen da mutanen gundumomin Batsari, da Dan-Musa, da Kankara da Wagini da sauransu wuraren da abun ya shafa suka samu kansu a ciki.
Sakataren masarautar Bello M Ifo shi ne ya fitar da ita, tare da shaida wa jama’a cewa sakamakon halin da suka samu kansu a ciki na alhini da jimami.
A wannan karon masarautar ta yanke shawarar a wannan karon ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba a baya.
Bello ya ce Mai-martaba sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman, da majalisar masarautar ne suka ga dacewar dage duk wasu shagulgula don nuna alhini kan abin da ya samu jama’arsu.
A karshen sanarwar ta ce za a je sallar idi kamar yadda aka saba, da yin addu’o’in neman zaman lafiya ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.