Home Labaru Kafofin Sadarwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Saki N30bn Na Bunkasa Yada Shirye-Shirye

Kafofin Sadarwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Saki N30bn Na Bunkasa Yada Shirye-Shirye

282
0

Hukumar kula da kafofin sadarwa ta Najeriya NBC, ta ce gwamnatin tarayya na yin dukkanin mai yiwuwa wajen sakin naira billiyan 30 da za a yi amfani dasu wajen bunkasa yada shirye-shirye na zamani, Digital Switch Over a turance.
Babban daraktan hukumar Ishaq Kawu, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Legas.
Ya ce ana sa ran sakin kudaden ne wadanda daga baya za a biya daga cikin abubuwan da aka samu na yada shirye-shiryen a cikin kashi biyu inda za a fara da bada naira billiyan 15.
Kawu ya ce hukumarsa ta shirya tsaf domin ganin an gudanar da ayyukan yadda ya kamata.
Ya kara da cewa hukumar ta riga ta kafa dukkanin kayayyakin aiki a wuraren masu yawan jama’a da suka kamata a fara dasu.
A karshe ya ce hukumar na tattaunawa da wani kamfani na kasar Koriya ta kudu da zai samar da na’urorin da mutane za su rika amfani dashi wajen kamo tashoshin da suke so.