Home Labaru An Samar Da Dokar Kisa Kan Masu Sace Jama’a A Katsina

An Samar Da Dokar Kisa Kan Masu Sace Jama’a A Katsina

310
0

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya sanya hannu kan dokar Penal Code da aka yi kwaskwarima wacce ta bayyana satar jama’a da shanu a matsayin manyan laifukan da suka cancanci hukuncin kisa.
Dokar ta kuma amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu yi wa mata fyade.
A yayin gabatar da jawabi, Gwamna Masari ya ce, jihar Katsina na fama da matsalar tsaro, abinda ya sa aka yi wa dokokin jihar kwaskwarima.
Haka zalika Gwamnan ya bayyana fatan cewa, matakin da suka dauka a yanzu, zai tsawatar da mutanen da ke da shawa’ar shiga harkar sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa.