Home Labaru Shugaba Buhari Ya Ƙaddamar Da Aikin Haƙo Man Fetur a Arewacin Najeriya

Shugaba Buhari Ya Ƙaddamar Da Aikin Haƙo Man Fetur a Arewacin Najeriya

58
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin
haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin
Bauchi da Gombe.

Yayin ƙaddamarwar, shugaba Buhari ya umurci kamfanin mai na NNPCL ya yi duk mai yiwuwa a hurumin da doka ta ba shi, domin tabbatar da sun janyo masu zuba jari domin bunƙasa sarrafa man fetur a Arewacin Nijeriya.

Shugaba Buhari, ya ce ya tattauna da gwamnonin Bauchi da Gombe, inda su ka tabbatar ma shi cewa za su bada haɗin kai domin ci-gaba da aikin bunƙasa haƙo man.

Daya daga cikin manyan jami’an kamfanin NNPC da ke kula da inda kamfanin ke zuba jari Bala Wunti, ya ce an gano aƙalla sama da ganga biliyan ɗaya ta ɗanyen man fetur a ƙarƙashin ƙasa.

Bala Wunti ya kara da cewa, ana fatan gina matatar man fetur da kamfanonin samar da taki da kuma iskar gas, kuma matatar man da ake fatan ginawa za ta riƙa sarrafa sama da ganga dubu100 a kowace.