Home Labaru Fasinjoji 17 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Abuja

Fasinjoji 17 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Abuja

23
0

Kimanin fasinjoji 17 su ka kone kurmus, bayan motar su da ta taso daga jihar Gombe zuwa jihar Lagos ta yi hatsari.

Rahotanni sun ce, mummunan hatsarin ya auku ne tskanin babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Daya daga cikin mutanen da su ka shaida lamarin Kabiru Garba, ya ce motar kirar Toyota Hiace ta ci karo ne da wata katuwar motar dakon kaya kusa da marabar Yaba a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Ya ce motar kirar Bas ce ta manno a guje ta ci karo da katuwar motar ta baya, lamarin da ya sa ta kama da wuta nan take.

Tuni dai jami’an kwana-kwana sun isa inda hatsarin ya auku domin kashe wutar da ta tashi, yayin da a gefe guda jami’an hukumar kiyaye hadurra ke aikin ceto.