
Gobara ta tashi a wata masana’anta da ke yankin Henan na China inda ta hallaka mutum 36.
Hakama wasu mutane biyu sun bata, sakamakon yadda wutar ke ci babu kakkautawa a masana’antar da ke yankin adana kayan kimiyya da fasaha a birnin Anyang.
Kafar yada labaran yankin, ta rawaito cewa tuni aka kama wasu da ake zargi da kunna gobarar.
Tashin gobara a masana’antu a China ba sabon abu ba ne, ana kuma zargin gwamnati da gaza daukar kwararan tsaro domin kaucewa hakan.
You must log in to post a comment.