Home Labaru Shugaba Buhari Ma Ya Cancanci Samun Kyautar Nobel – Garba

Shugaba Buhari Ma Ya Cancanci Samun Kyautar Nobel – Garba

292
0
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai
Garba Shehu, Mai Ba Wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari Shawara Na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce kyautar zaman lafiya ta Nobel da aka karrama firayin ministan Habasha Aby Ahmed da ita abin alfahari ce ga Afirka, ta yadda firayin ministan ya iya sasanta rikicin da ke tsakanin kasar sa da makwafciyar ta Eritrea.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, aka ba Abiy Ahmed kyautar, sakamakon kokarin sa na wanzar da zaman lafiya tsakanin kasar sa Habasha da makwafciyarta Eritrea, da kuma rawar da ya taka wajen sasanta rikicin Sudan tun bayan hawan sa karagar mulki.

Shugaba Buhari, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin alfahari ga Afirka baki daya, ya ce shi ma ya cancanci samun irin wannan kyauta.

Ya ce kyautar gagarumin ci-gaba ne ga nahiyar Afirka ta fuskar zaman lafiya da dorewar kwanciyar hankali, sai dai mai Magana da yawun sa Garba Shehu ya ce, shugaba Buhari ma ya cancanci ya samu irin wannan kyautar saboda rawar da ya taka wajen kawo karshen rikicin al’ummar Tibi da Jukun. Garba Shehu, ya ce dalilin da ya sa Nijeriya ba ta samun irin wannan kyautar shi ne, rashin rubuta kasar da kuma haska irin kokarin da ta ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin jama’a.