Home Labaru Ba Ni Da Hannun Jari A Kamfani Wutar Lantarki Na KAEDCO –...

Ba Ni Da Hannun Jari A Kamfani Wutar Lantarki Na KAEDCO – Namadi

319
0
Namadi Sambo, Tsohon mataimakin shugaban kasa
Namadi Sambo, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Namadi Sambo, ya ce ba ya hannun jari a kamfanin raba wutan lantarki na KAEDCO.

Namadi Sambo ya bayyana haka ne, domin karyata wata jarida da ta wallafa labarin cewa ya na da hannun jari a kamfanin na KAEDCO.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi Sambo ya karyata labarin, sannan ya yi kira ga jama’a su yi watsi da zancen saboda babu gaskiya a cikin sa.

Ya ce ko a lokacin da ya shugabanci kwamitin saida kadarorin gwamnat yayin da ya ke mataimakin shugaban kasa, sun yi aiki ne a cikin tsoron Allah da ci-gaban kasa, kuma kowa ya shaida an kuma yaba. Namadi Sambo ya cigaba da cewa, jaridar da ta wallafa labarin ba ta yi ma shi adalci ba, don haka ya bukaci editocin jaridar su gaggauta rubuta takardar ba shi hakuri su kuma janye labarin nan da tsawon mako daya.