Home Labaru Rikicin Tibi Da Jikun: An Yi Zaman Samun Maslaha A Birnin Jalingo...

Rikicin Tibi Da Jikun: An Yi Zaman Samun Maslaha A Birnin Jalingo Na Jihar Taraba

228
0

An yi wani gangamin gamayyar kungiyoyin Arewacin Nijeriya a jihar Taraba, domin samar da sulhu tsakanin kabilun Tibi da Jikun.

Rikici tsakanin kabilun biyu dai ya ki ci ya ki cinyewa, kuma an dade ana irin wannan zama domin samar da sulhu amma abin ya ci tura.

Gammayar kungiyoyin ta fara ne da hada matasan kabilu biyu ta hanyar hada su a kan teburi guda, domin tattaunawa irin ta fahimta a birnin Jalingo na jihar Taraba, lamarin da ya kai ga har sun cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewacin Nijeriya Ashiru Sherrif, ya ce sun yarda gaba daya cwa rikicin ba ya da amfani a cikin alumma.

Ya ce wannan rikici ya sa an hallaka mutanen da ya kamata a ce nan gaba su ke rike da kasa.

A karshe ya ce sun cimma matsaya, inda duk kabilun biyu sun amince a kira manya-manyan shugabannin su na addini da sarakuna a zauna domin tabbatar da an samu maslaha ta karshe da za a kawo karshen wannan rikici.