Hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya, ta ce ta yi nasarar hana sama da bakin-haure 1,000 shiga Nijeriya makonni kadan bayan rufe iyakokin kan tudu ciki har da mutanen da su ka fito daga nahiyar Asiya.
A cewar hukumar, aikin hadin-gwiwar da hukumar kwastam da kuma sojoji da sauran jami’an tsaro wajen sa ido a kan iyakokin Nijeriya, su na taimakawa wajen dakile ta’addanci.
Shugaban
hukumar shige da fice Muhammad Babandede, ya ce Nijeriya ta ba wadanda su ka
shigo ba bisa ka’ida ba wa’adin su yi rijista nan da farkon shekara mai zuwa.














































