Home Labaru Ra’ayi: Masu Kukan Yunwa A Nijeriya Na Rashin Kunya Ne – Nanono

Ra’ayi: Masu Kukan Yunwa A Nijeriya Na Rashin Kunya Ne – Nanono

232
0
Sabo Nanono, Ministan Harkokin Noma Da Raya Karkara
Sabo Nanono, Ministan Harkokin Noma Da Raya Karkara

Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara Sabo Nanono, ya ce Nijeriya ta na noma abincin da zai ishi kowa har ma ta aika da shi kasashen da ke makwaftaka da ita.

Da ya ke jawabi a wajen taron Ranar Abinci ta Duniya a Abuja, Ministan ya ce ‘yan Nijeriya su na noma abincin da za su iya ciyar da kan su, don haka babu wata yunwa a Nijeriya, kuma masu korafin cewa ana fama da yunwa a Nijeriya dariya su ke ba shi.

Ana dai gudanar da bikin murnar zagayowar Ranar Abinci ta Duniya ne a kowace rana 16 ga watan Oktoba, domin tunawa da ranar da aka kafa Kungiyar Abinci da Ayukan Gona ta Majalisar Dinkin Duniya cikin shekara ta1945.

A cewar Nanono, abinci arha ya ke yi takab a Nijeriya idan aka kwatanta da wasu kasashe, domin ko a Kano za ka iya cin abinci da naira 30 kacal kuma ka koshi.

Ya ce gwamnatin tarayya ta yi tunanin rufe kan iyakokin ta ne, saboda kasashe makwafta sun maida ta wurin jibge kayayyaki da shinkafar da lokaci ko wa’adin cin ta ya wuce.