Home Labaru Tsaro: Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari

Tsaro: Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari

201
0
Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari
Kada Ku Tausayawa ‘Yan Bindiga- Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dakarun sojin sama na Najeriya dake Jihar Katsina kada su sassautawa ‘yan bidinga domin sun dade suna muzgunawa jama’a.

Karanta Wannan: Samar Da Tsaro: Buratai Ya Yabawa Jami’an Soji

Shugaban kasa Buhari, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake   jawabi ga sojojin, wadanda suka hada da manyan sojoji 15 da kuma dakarun sojoji  a  bataliya ta da sojojin saman dukkanin su a karkashin rundunar Operation Sharan daji.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a matsayin sa  na babban kwamandan Askarawan Najeriya, akwai  yakinin cewa za a iya kawao karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Ya ce baya bukatar sojojin su dagawa kowa kafa, saboda ba a bukatar sassauci daga bangaren tsaro, kuma su yi bincike, sannan su tabbatar sun ga bayan su.

Ya ci gaba da cewar Najeriya  na bukatar zaman lafiya, duk da cewar damina ta kankama kuma an sami abinci daidai gwargwado, amma abu mafi a’ala shi ne a  sami zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban kasa wanda ya sami rakiyar gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari zuwa filin jirgin Umaru Musa ‘Yar Adua Katsina, ya shaidawa sojoji cewa gwamnatin tarayya a shirye take wurin bada duk wata gudunmuwa ga jami’an tsaro domin samar da tabbataccen zaman lafiya.