Home Labaru Shehu Sani Ya Ce A Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin Ma’Aikatan Gwamnati

Shehu Sani Ya Ce A Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin Ma’Aikatan Gwamnati

16
0

Tsohon dan majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya tun da an gaza sanya su a jerin ‘yan ta’adda.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na  Twitter, Sanatan ya koka da yadda ‘yan bindiga ke hallaka Bayin Allah a wuraren ibadun su, amma an ki ayyana su a jerin ‘yan ta’adda a Nijeriya.

Ya ce ‘yan bindigan sun kashe musulmai masu ibada a masallatai a jihohin Neja da Katsina, sun kuma hallaka kiristoci a cocin su a jihar Kaduna.

Shehu Sani, ya ce idan gwamnati ba za ta iya ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba to sai ta ayyana su a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya.