Home Labaru Baba-Ahmed Ya Bayyana Irin Dan Takarar Da Yankin Arewa Zai Goyi Baya

Baba-Ahmed Ya Bayyana Irin Dan Takarar Da Yankin Arewa Zai Goyi Baya

24
0

Mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa Hakeem Baba-Ahmed, ya ce yankin arewacin Nijeriya zai zabi dan takara mai nagarta ne daga kowanne yanki a shekara ta 2023.

Baba-Ahmed, ya ce yankin arewa ba zai lamunci ko kuma saurari dan takarar da aka fitar ta hanyar amfani da bangaranci ko addini ba.

A yayin tattaunawa da manema labarai, ya ce halin da Nijeriya ke ciki a yanzu ba a bukatar shugaban da za a samar ta hanyar amfani da bangaranci ko kuma barazanar rabewar kasar nan.

Ya ce duk wani yunkurin mamaye ofishin shugaban kasa ta hanyar tada tarzoma ya na iya kawo barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasar nan.

Hakeem Baba-Ahmed, ya ce yankin arewa ba zai girgiza da duk wata barazanar raba kasar nan kafin zabe mai zuwa ba, ya na mai jan hankalin ‘yan awaren Biafra su daina tada tarzoma a yankin su.