Home Labaru Mafi Muni A Cikin Mulkin Soja Ya Fi Sauki A Kan Na...

Mafi Muni A Cikin Mulkin Soja Ya Fi Sauki A Kan Na Shugaba Buhari – Ortom

12
0

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya sake sukar gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari, inda ya ce duk lalacewar gwamnatin sojoji ta fi mulkin jam’iyyar APC sauki da jin daɗi.

Samuel Ortom ya bayyana haka ne, yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Makurɗi, jim kaɗan bayan komawar sa daga taron jam’iyyar PDP na ƙasa.

Gwamna Ortom ya ƙara da cewa, sakamakon da kowa ya gani a babban taron PDP na ƙasa, babbar alama ce da ke nuni da cewa jam’iyyar ta shirya karbar mulki a shekara ta 2023.