Home Labaru Shawara: Buhari Ya Bukaci Shugaban Habasha Ya Tabbatar Da Zaman Lafiya a...

Shawara: Buhari Ya Bukaci Shugaban Habasha Ya Tabbatar Da Zaman Lafiya a Ƙasarsa

6
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugaban Habasha Abiy Ahmed, da ya ci gaba da lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a ƙasarsa da ke Gabashin Afirka.

Buhari ya yi kiran ne a birnin Addis Ababa yayin da yake halartar bikin rantsar da Shugaba Ahmed a wa’adi na biyu.

Wata sanarwa da Fadar Shugaban ta fitar a Ranar Litinin din da ta gabata ta ambato Buhari na cewa “Najeriya za ta taimaka wajen tabbatar da haɗin kai da kuma ‘yancin Ethiopia”.

Yace “suna sane da tarin ƙalubalen da ke gaban kasar ta Habasha kuma zasu ƙarfafa wa kowane ɓangare gwiwa da su haɗu waje guda domin neman haɗin kai da cigaba da kuma zaman lafiyar Ethiopa.

Ƙasar Habasha ta shafe shekara kusan biyu tana cikin yaƙi, yayin da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Abiy Ahmed ke fafutikar murƙushe ‘yan tawaye a yankin Tigray da ke son ɓallewa daga ƙasar.