Home Labaru Gidajen Holewa A Legas Na Damun Dattawa Da Hayaniya

Gidajen Holewa A Legas Na Damun Dattawa Da Hayaniya

6
0

Gwamnatin Jihar Legas, ta gargaɗi gidajen holewa da wuraren shan giya su rage damun mutane da hayaniya ko su fuskanci hukunci.

Hukumomi sun ce, dattawa mazauna unguwar Lekki sun sha kai musu kuka game da hayaniyar da su ka ce tana shafar lafiyar su.

A wata sanarwa da gfwamnatin jihar ta fitar, ta ce hayaniyar ta na faruwa ne a kowane farkon dare har zuwa asubahi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni an kama mutane a wasu wurare da ke Lekki, inda jami’an tsaro su ka rufe wurin holewa na Prest Jazz da aka samu su na amfani da manyan lasifiƙoƙi.