Home Labaru Zaben 2023: Sule Lamido Yace Ba Za Su Lamunci PDP Ta Kai...

Zaben 2023: Sule Lamido Yace Ba Za Su Lamunci PDP Ta Kai Takara Kudu Ba

6
0
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Sule Lamido, ya ce ba za ta yiwu ba, a mika wa yankin kudancin kasar takarar shugaban kasa a jam'iyyar a kakar zaben 2023 saboda kawai son kai ba.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Sule Lamido, ya ce ba za ta yiwu ba, a mika wa yankin kudancin kasar takarar shugaban kasa a jam’iyyar a kakar zaben 2023 saboda kawai son kai ba.

Tsohon gwamnan ya ce ba laifi bane idan an yi hakan saboda tunanin zaman lafiya da kuma son farfado da tasirin jam’iyyar a yankin arewa, wadda ake sa ran za ta karbi mukamin shugabancin jam’iyyar.

Sule Lamido ya kara da cewa ”ai an taba yin haka a PDP, aka dauko Obasanjo aka ce shi kadai zai yi takara, amma ka ga ai ba dole aka yi wa mutane ba, an yi ne domin ci gaban kasa da kuma son tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki”

A wani taron da gwamnonin kudancin Najeriya suka gudanar a watan Yuli, sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.

Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara a fadin kasar, inda kungiyar dattawan arewacin kasar ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zaɓen wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ƙasar a zaben 2023.