Home Labaru Shari’ar Zabe: Atiku Ya Lalubo Ma’aikatan Hukumar Zabe Cikin Masu Yi Masa...

Shari’ar Zabe: Atiku Ya Lalubo Ma’aikatan Hukumar Zabe Cikin Masu Yi Masa Shaida A Kotu

205
0

Akalla mutane 12 da su ka yi wa hukumar zabe aiki a zaben shekara ta 2019 ne za su tsaya wa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a kotun da ke sauraren kararrakin zabe.

Wata majiya ta ce wasu Ma’aikatan hukumar zabe da aka yi amfani da su a zaben shekara ta 2019, za su je gaban kotu su rantse cewa sun yi aiki da na’urar zamani wajen aika sakamakon zaben shugaban kasa.

Atiku Abubakar dai ya na korafin cewa shi ya lashe zaben shekara ta 2019 kamar yadda alkaluman da ke cikin na’urorin ajiyar kuri’un da hukumar zabe ta ke amfani da su su ka nuna, inda ya ce a zahiri shi ya lashe zaben da kuri’u miliyan 18 da dubu 356 da 732.

Sai dai hukumar zaben ta karyata cewa ta yi aiki da na’urori wajen tattara kuri’u a zaben shekara ta 2019, lamarin da ya sa  Atiku Abubakar ya nemo wadanda su ka yi aiki da hukumar zuwa kotu su rantse da cewa an yi amfani da na’urorin.

Atiku Abubakar, ya ce wani dan cikin-gidan hukumar zaben ne ya fito masa da sakamakon zaben daga cikin na’urorin hukumar, yayin da Atiku Abubakar ya bayyana lambobin na’urorin domin ya kara wa hujjar sa karfi a gaban kotun.