Home Labaru Difilomasiyya: Nijeriya Da Ghana Sun Hada Kai Domin Magance Laifuffukan Yanar Gizo

Difilomasiyya: Nijeriya Da Ghana Sun Hada Kai Domin Magance Laifuffukan Yanar Gizo

235
0

Gwamnatin tarayya, ta daura damarar hadin gwiwa da gwamnatin kasar Ghana domin magance miyagun laifuffuka ta hanyar yanar gizo don bunkasa ci-gaba da kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Jakadan kasar Ghana a Najeriya Alhaji Bashir Bawa ya bayyana haka a birnin Calabar, yayin ziyarar shugaban hukumar shige da fice na jihar Cross River Mista Felix Uche.

Alhaji Bawa ya lura cewa, hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki na kasashen biyu, zai taimaka tare da taka muhimmiyar rawar gani wajen magance miyagun laifuffukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.

Ya ce bisa ga shimfida tsari da kyawawan dokoki wajen tarayya ta daura sulke a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, zai magance tare da kawo sauki na aukuwar miyagun laifuffuka kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Jakadan na Ghana, ya kuma yaba wa hukumar shige da fice ta Nijeriya, sakamakon kyakkyawar dangantakar da ke ci-gaba da habbaka zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin kasashen biyu da ke makotaka da juna.

Leave a Reply