Home Labaru Shari’ar IPOB: Lauyan Nnamdi Kanu Ya Bukaci Hukumar DSS Ta Biya Shi...

Shari’ar IPOB: Lauyan Nnamdi Kanu Ya Bukaci Hukumar DSS Ta Biya Shi Diyyar Naira Miliyan 50

55
0

Maxwell Opara, daya daga cikin lauyoyin Nnamdi Kanu, Shugaban haramtacciyar kungiyar ’yan a-waren Biyafara (IPOB), ya maka Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a kotu kan zargin cin zarafinsa.

A takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1018/2021, lauyan ya yi zargin cewa ya fuskanci cin zarafi iri-iri a lokacin da ya ziyarci Kanun a wurin da DSS take tsare da shi a a ranar 30 ga watan Agusta, 2021.

Barista Maxwell Opara, ya lissafo hukumar ta DSS da Shugabanta a cikin wadanda yake kara, yana roki kotun sa su biya shi Naira miliyan 50 a matsayin diyyar hakkinsa da aka take.

Yana kuma rokon kotun da ta bayar da umarnin wucin gadi da zai hana DSS daga ci gaba da yi wa hakkinsa na dan Adam katsalandan.

Maxwell na Nnamdi Kanu ya kuma bukaci kotun ta hana kowa tsangwamar sa ko yi wa ’yancinsa na watayawa kutse a duk lokacin da ya ziyarci wanda yake karewar.

Bugu da kari, lauyan na bukatar kotun ta tilasta wadanda yake kara su ba shi hakuri a manyan jaridun Najeriya akalla guda biyu.

Lauyan ya ce matakin da DSS ta dauka a kansa ya saba da tanade-tanade sashe na 34 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Sai dai ya zuwa yanzu kotun ba ta tsayar da ranar fara sauraron karar ba.