Home Labaru Ta’addanci: An Yi Garkuwa Da Mutum 18 A Jihar Kaduna

Ta’addanci: An Yi Garkuwa Da Mutum 18 A Jihar Kaduna

56
0

Akalla mutum 18 ne aka fargabar ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a unguwar Keke da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

An rawaito cewa ’yan bindigar sun shiga unguwar ce da misalin karfe 12 na dare, suna harbi a iska.

Wani wanda ya gane wa idonsa, ya bayyana cewa ’yan masu yawan gaske ne suka shiga unguwar, sannan suka sace mutum 18.

Wakilinmu ya bayyana cewa tuni jami’an ’yan sanda suka isa yankin don tsananta bincike kan faruwar lamarin.

Sai dai har yanzu babu wani tabbacin faruwar lamarin daga bangaren rundunar ’yan sandan jihar.