Home Home Shari’a: Kotu Ta Umarci DSS Ta Biya Sowere Diyyar Kamen Sa Kan...

Shari’a: Kotu Ta Umarci DSS Ta Biya Sowere Diyyar Kamen Sa Kan Zanga-Zangar Revolutionnow

25
0
Babbar kotun tarayya Abuja, ta ayyana kamun da aka yi wa mawallafin jaridar Sahara kuma jagoran zanga-zangar juyin-juya hali Omoyele Sowere a matsayin haramtacce, tare da bukatar biyan sa diyyar cin zarafin da aka yi ma shi.

Umarnin alkalin kotun dai ya na zuwa ne, makonni uku bayan wata babbar kotu a karkashin jagorancin mai shari’a Chikere Anwuli ta Umarci hukumar tsaro ta DSS ta biya Sowore naira miliyan biyu sakamakon karbe ma shi wayar hannun sa yayin da aka kama shi.

A hukuncin kotun, alkalin ya kuma bada umarnin a saki wasu mutane biyu da ake zargin su na da hannu wajen mara wa Sowore baya a zanga-zangar da ya yi wa lakabi da #RevolutionNow a Turance.

Tuni dai lauyoyin Sowore da su ka hada da Marshar Abubakar da Femi Falana, sun ayyana hukuncin a matsayin bayyanar gaskiya kuma abin kunya ga hukumar tsaro ta DSS.